Posts

Showing posts from April, 2017

EFCC ta kama tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu

Image
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC), ta kama tsohon gwamnan jihar Neja Dr Mu'azu Babangida Aliyu kan zargin cin hanci da rashawa da halatta kudaden haram. Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa da BBC cewa hukumar tana rike da tsohon gwamnan. "Yana hannunmu kuma muna cigaba da yi masa tambayoyi," in ji mista Uwujaren. Sai dai bai yi karin haske kan abin da ake tuhumur tsohon gwamnan da aikata wa ba. Hakazalika bai bayyana lokacin da hukumar za ta gurfanar da Dr Aliyu a gaban kotu ba. Tsohon gwamnan na Neja ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga shekarar 2007 zuwa ta 2015. Kuma ya fadi takarar kujerar majalisar dattawa da ya nema a zaben 2015.