Posts

An Cimma Matsayar Sake Nazari Kan Mafi Karancin Albashi A Najeriya

Image
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya, Ayuba Wabba ya ce an cinmma matsaya tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar domin sake duba batun kara yawan mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata a kasar. Wabbba ya bayyana haka ne yayin zantawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN a birnin Abuja. Shugaban kwadagon ya ce nan bada dadewa ba za’a kafa kwamiti na musamman mai wakilai daga bangaren gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da kuma bangaren kungiyar kwadagon da zasu tantance tare da cimma matsaya kan yawan albashin mafi karanci. A baya dai kungiyar kwadagon ta gabatarwa gwamnatin Najeriya bukatar kara yawan mafi karancin albashin ma’aikata a kasar zuwa naira dubu hamsin da shidda.

Gwamnatin Najeriya ta amince da daukar sabbin 'yan sanda 10,000 duk shekara

Image
Gwamnatin Najeriya ta bawa rundunar ‘yan sandan kasar, daukar sabbin jami’ai dubu goma a duk shekara, domin kawo karshen rashin yawan jami’an tsaron da kasar ke fuskanta. Babban Sifeton ‘yan sandan kasar Ibrahim Idris ya tabbatar da samun cigaban, yayinda yake jagorantar wani taro da manyan jami’an ‘yan sanda a birnin Abuja. Sifeto Janar Idris, ya ce Karin ya zama tilas domin samun nasarar murkushe aikata miyagun laifuka a kasar. Ya ce kara yawan jami’an ‘yan sandan zai canza alkalumman da ke aiki a Najeriya, da ya nuna cewa dan sanda guda ne ke lura da mutane 400 a kasar. A bangaren majalisar kasar kuwa, Sifeto Janar Idris ya bukaci da ta gaggauta sanya hannu kan kudurin da aka gabatar mata na kara yawan kudaden da ake warewa hukumar ‘yan sandan kasar.

Allahu Akbar Allah Ya Yi Wa Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Mazabar Mashi A Jihar Katsina, Hon Sani Mashi Bello Rasuwa

Image
Marigayin mai shekaru 51, ya rasu ne a yau Laraba, sakamakon rashin lafiya da ya yi.

Wata Kotu a birnin Kano ta mallakawa Gwamnatin Nijeriya Dala miliyan kusan 10 da aka samu a gidan Andrew Yakubu da kuma wasu Fam 74,000.

Image

Hotuna: An Yi Sahu Tare Da Yin Sallah Da Adduoin Alkhairi Ga Gwamnatin Shugaba Buhari A Kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Kano

Image

Hotuna: Masu Zanga-Zangar Goyon Bayan Shugaba Buhari A Yau, Laraba, 15 Ga Watan Fabrairu A Kan Zaria Road Da Ke Kano

Image

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a jihar Neja a yau Talata.

Image
Kakakin tsohon mataimakin shugaban kasan Paul Ibe ya ce Atiku ya ziyarci Babangida ne domin ya mika gaisuwarsa ganin cewa kwanan nan ne ya dawo daga asibiti. Babangida ya dawo daga kasar Switzerland ranar Lahadi bayan makonni bakwai da ya yi a kasar ya na ganin likitoci. Atiku ya koma garin Minna ne musamman domin ziyarar tsohon shugaban kasan saboda baya kasa a lokacin da ya je ta’aziyar rasuwar tsohon gwamnan jihar Abdukadir Kure a watan Janairun da ya gabata. Daga karshe Paul Ibeh ya yi kira ga mutane da kada su yi ma wannan ziyara ta Atiku da wata fassara daban.