An Cimma Matsayar Sake Nazari Kan Mafi Karancin Albashi A Najeriya
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya, Ayuba Wabba ya ce an cinmma matsaya tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar domin sake duba batun kara yawan mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata a kasar.
Wabbba ya bayyana haka ne yayin zantawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN a birnin Abuja.
Shugaban kwadagon ya ce nan bada dadewa ba za’a kafa kwamiti na musamman mai wakilai daga bangaren gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da kuma bangaren kungiyar kwadagon da zasu tantance tare da cimma matsaya kan yawan albashin mafi karanci.
A baya dai kungiyar kwadagon ta gabatarwa gwamnatin Najeriya bukatar kara yawan mafi karancin albashin ma’aikata a kasar zuwa naira dubu hamsin da shidda.
Comments