An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya
Hukumomi a Najeriya sun ce sun gano wasu makudan kudade da aka sace daga asusun gwamnati da yawansu ya kai dala miliyan dari da hamsin, da kuma wata naira biliyan takwas.
Ministan yada labarai na kasar, Alhaji Lai Mohammed, a cikin wata sanarwa, ya ce an gano kudaden ne daga wajen mutane uku, sakamakon wasu da suka tona asirinsu.
Ministan ya ce kudaden ba sa daga cikin fiye da dala miliyan tara da aka gano a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na kasar NNPC, Andrew Yakubu, wanda shi ma wani ne ya tona musu asiri.
Alhaji Lai Mohammed ya ce daga cikin kudin, dala miliyan dari da talatin da shida da dubu dari bakwai, an gano su ne a wani banki a kasar, an an boye su ne da wani suna na bogi.
Ya ce naira biliyan bakwai kuma da dala miliyan goma sha biyar, an same su ne daga wurin mutun guda, sai kuma wata naira biliyan daya da aka samu daga wajen wani mutun guda shima.
Ministan ya ce wannan bankadowa da aka yi, ta kara jaddada matsayarsu a baya, cewa an tafka babbar sata a zamanin tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan.
Ya kuma ce bisa dukkan alamu, tsarin gwamnatin kasar na bayar da tukwici ga wadanda suka tona asirin mutanen da ake zargi da wawure kudaden gwamnati ya fara tasiri.
"Dududu wannan tsari bai wuce wata biyu da bullo da shi ba, amma 'yan Najeriya sun fara ganin tasirin shi, yadda 'yan tsirarun mutane suka wawushe kudaden kasa" Lai Mohammed ya ce.
Ministan ya ce ya na tababar ace akwai wata kasa a duniya da tattalin arzkinta ba zai yi kasa ba idan ta fuskanci irin wannan babbar satar kudaden gwamnati.
A saboda haka Ministan ya bukaci 'yan Najeriya da su ke da bayanai game da wadanda suka saci dukiyar kasa da su tona musu asiri, inda ya ce akwai tukwici da ya kama daga kashi biyu da rabi zuwa kashi biyar cikin dari na dukiyar da aka gano.
Ministan bai sanar da sunayen mutane ukun da aka gano kudaden daga wurin su ba.
Yaki da cin hanci da rashawa yana daya daga cikin manyan alkawuran da shugaban Najeriya, Mohammadu Buhari ya yi wa jama'a kafin a zabe shi.
Comments