Cinikin makamai ya karu a duniya
Wani sabon rahoto da a gudanar, ya bayyana cewa ba a taba samun wani lokaci da aka yi cinikin makamai a duniya kamar dan tsakanin nan ba tun bayan yakin Duniya na biyu.
Kwararru a cibiyar Stockholm Internation Peace Research da suka fitar da sakamakon binciken, sun ce yawan makaman da aka yi cinikinsu tsakanin shekarar 2012 zuwa bara, ya tashi da kashi 8 cikin dari idan aka kwatanta da shekaru biyar da suka wuce.
Kasashen gabas ta tsakiya da kasashen Golf su ne suka fi sayan makamai a wannan lokacin, ya yin da a cikinsu Saudiyya ta fi kowacce sayan makamai, sai kuma kasar India.
Rahoton ya karkare da cewa kasashe biyar a duniya su ke fitar da kashi 75 cikin 100 makaman, wato Amurka, da Rasha, da China, da Faransa sai kuma Jamus.
Comments