Mata Sun Yi Gangami A Kano Sakamakon Yawan Satar Yara
Daruruwan matane suka fito domin gudanar da zanga-zanga da nuna fushinsu akan yadda gwamnati ta nuna halin ko in kula da yadda a ke ta sace musu yara a unguwannin su da ya hada musamman da Hotoro, Kawo, Kawon Mallam da Kawon Maigari.
Matan sun fito kan titunan birnin na Kano ne inda suka dunguma zuwa gidan gwamnatin jihar domin mika sakon su ga gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.
Ko da yake ba suyi dace da hakan ba domin basu samu ganin gwamnan jihar ba, kakakin gwamnan Salihu Yakasai yace gwamnati ba za tayi kasa kasa ba wajen ganin ta dakatar da wannan mummunar aiki ya ci gaba a jihar.
“Gwamnati ta dauki matakai domin dakatar da matsalar satan yara da akeyi a jihar.”
Jagoran matan Halima Abubakar ta ce sun sanar wa gwamnati cewa akwai wata mata da take sace yara a unguwanninsu amma gwamnati da jami’an tsaro sun nuna halin ko in kula akai.
Comments