Trump: Za Mu Yi Aiki Tare Da Buhari
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tattauna da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari na Najeriya,ta waya, a ranar Litinin, inda suka tattauna batutuwa da dama.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Garba Shehu wanda ya wallafa yadda tattaunawar shugabannin biyu ta kasance, ya ce, mista Trump ya yaba wa Buhari kan kokarinsa wajen 'yanto 'yan matan Chibok guda 21.
Har wa yau, Donald Trump, ya ce, shugaban na Najeriya ya cancanci yabo dangane da yaki da ta'addanci.
Gwamnatin Muhammadu Buhari dai ta ce ta samu nasara wajen tarwatsa mayakan Boko Haram.
Wannan ne ya sa shugaban na Amurka neman hadin-kan Buhari domin yin aiki tare musamman wajen yakar ta'addanci.
Daga karshe, shugaba Trump ya nemi Buhari da ya ci gaba da zartar da ayyukan alkairi da yake yi domin ciyar da Najeriya gaba
Comments