Tuface ya soke Zanga-zangar da yake shirin gudanarwa

Shahararren mawakin nan Tuface Idibia ya sanar da soke zanga-zangar da yake shirin gudanar wa ranar litini 6 ga watan Faburairu.
Tuface ya sanar da hakanne a wata sako da ya rubuta a shafinsa na Instagram inda ya ce yayi hakanne saboda tsaro.
Kungiyoyi da dama sun nuna rashin amincewarsu da shirin zanga-zangar da mawakin ya shirya.
Shugaban kungiyar mawakan jam’iyyar APC Haruna Ningi ya ce kungiyarsa ba ta goyon bayan shirin zanga-zangar, haka kuma Kungiyar ina tare da Buhari wato ‘#IstandwithBuhari’ ta sanar da cewa ita ma ta shirya fitowa zanga- zanga domin nuna goyon bayan ta ga shugaba Muhammadu Buhari.
Tuface ya shirya wata zanga-zanga domin nuna bacin ransa da kira ga gwamnati da ta kawo wa mutane dauki akan irin wahalar da ake fama dashi a kasa Najeriya.
Rundunar ‘yansanda ta shawarci mawaki Tuface da ya dakatar da fitowa zanga zangar da ya ke shirin yi domin nuna rashin jin dadinsa akan mulkin shugaba Muhammadu Buhari saboda tsaro.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya