Masu garkuwa da Jamusawa biyu a Najeriya Na Bukatar Naira Miliyan 60

Mutanen da suka yi garkuwa da wasu Jamusawa biyu a jihar Kaduna dake Najeriya sun gindaya sharudda kafin su sako Jamusawan da aka sace tun ranar Laraba data gabata.
Jamusawan biyu sun hada da Peter Breunig da Johannes Buringer wadanda aka sace a kauyen Jenjela dake karamar Hukumar Kagarko na jihar Kaduna inda suka tafi wajen aikin hakar ma’adinai.
Majiyoyin samun labarai na cewa masu garkuwa da su na bukatar kudi Naira miliyan 60 kafin su sako Jamusawan.
Ganau sun bayyana cewa sai da masu satan Jamusawan suka kashe wasu ‘yan kauyen biyu kafin su yi awon gaba da Jamusawan.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya