Bam Ya Kashe Wani Soja Da Yan Uwansa Biyu A Jihar Neja
Za’a iya cewa tsautsayi ne ta fada akan wani sojin Najeriya da ya tafi gida wajen ‘yan Uwansa bayan ya dan dauki hutu da ga filin daga a can jihar Barno.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja Bala Elkalla ya ce sojan ya zo ganin gida sai kuma Allah yayi ajalinsa na gida.
Yace hadarin ya faru a lokacin da sojan yake ba ‘yan uwansa labarin yadda suke yaki da Boko Haram a dajin Sambisa, tare da shi a wannan lokaci kuma akwai Bam din hannu wanda ya ke nuna musu dashi. Ana cikin haka ne fa sai Bam din ya tashi a tsakaninsu.
Da shi da wadansu ‘yan uwansa biyu suka mutu nan take.
Elkalla yace ba hari bane a ka kai karan kwana ne kawai.
Comments