Adama Barrow ya bayar da umarnin sakin fursunoni 171

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya bada umarnin sakin baki dayan fursunonin da ke tsare a gidajen yarin kasar, wadanda aka tsare ba tare da an gurfanar da su gaban shari’a ba saboda dalilan siyasa.
Barrow ya bada umarnin ne yayinda yake jaddada alkawarin da yayi na kawo karshen tauye hakkin dan adam da aka zargi gwamnatin Yahya Jammeh da aikatawa, a jawabin da ya gabatar bayan bikin kama aikinsa da ya gudana a birnin Banjul a ranar Asabar da ta gabata.
Jim kadan da bada umarnin, aka saki fursunoni 171, wadanda aka kama a zamanin gwamnatin Jammeh.
Shugaba Adama Barrow ya kuma za’a gudanar da sauye sauye a kundin tsarin mulkin kasar, zai kuma bayyana matakai na farko da za’a dauka a lokacin da zai gabatar da jawabinsa na farko ga zauren majalisar kasar.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya