Kamar yadda Faruk ya bayyana, a shafinsa na twitter, wadansu mutane da ba a san su ba, sun yi gaba da Sada Abu Gidado a jiya, A Katsina. 'Allah Ya bayyana shi, amin ya Rabbi'
1. Rage Kibar Jiki : Binciken masana ya tabbatar da cewa Kabeji yana rage wa wanda ke cinsa kiba. Don haka idan mutum ba ya so ya rika yin kibar wuce geji, ya lizimci cin kabeji. 2. Yana Kara Kaifin Basira: Kabeji cike yake da sinadarin ‘Bitamin K’ wanda shi ke kara wa mutum hazakar kwakwalwa da kuma fahimta. Haka kuma masanan sun ce Kabeji yana taimakawa wurin yi wa mai amfani da shi garkuwa daga cututtukan da suka shafi kwakwalwa. A nan kuma sun ce, jan Kabeji ya fi Kore yin wannan aiki. 3. Kara Wa Mutum Kyau: Ganyen Kabeji yana da sinadarin da ke sa fatar mutum ta rika sheki da kyau, sannan yana sa taushi da kyallin gashi, haka ma farcen mutum kan yi kyau. 4. Kabeji Na Cire Datti Da Warin Jiki: Masana sun tabbatar da cewa Kabeji na taimaka wa mutane wurin cire datti da warin jiki. Saboda sindarin ‘Bitamin C’ da ke cikinsa. Wanda yake garkuwa da wasu manyan cututtukan fata da kuma cututtukan sanyin kashi. 5. Kabeji Na Magani Da Garkuwa Ga Cutar Kansa: Kabej...
Wani likita a asibitin Makurdi Dr Martins Adejo ya gargadi mata da su yi taka tsantsan da saka takalman masu tsini domin ya na lahanta kashin bayan mutum. Likitan yace wadannan takalma na illata kashin baya wanda hakan ya kan lalata wasu sassan dake hade da kashin baya bayan illata kashin shi kansa. Ya kara da cewa takalma masu tsini na kawo matsala a kwiwwowi da gabobi da tafin kafa, sannan kuma yana raunana jijiyoyin dake tafiyar da jinni a jikin mutum. “ Idan mace ta nace da sa irin wadannan talkalma za ta samu matsala da jijiyoyin ta da kuma gabobin jikinta idan girma ya zo. Likita Adejo yace dalilin irin wadannan matsaloli da za’a iya samu zai iya kai ga mutum ya kamu da cutar hawan jinni da ciwon suga.
Hukumomi a Najeriya sun ce sun gano wasu makudan kudade da aka sace daga asusun gwamnati da yawansu ya kai dala miliyan dari da hamsin, da kuma wata naira biliyan takwas. Ministan yada labarai na kasar, Alhaji Lai Mohammed, a cikin wata sanarwa, ya ce an gano kudaden ne daga wajen mutane uku, sakamakon wasu da suka tona asirinsu. Ministan ya ce kudaden ba sa daga cikin fiye da dala miliyan tara da aka gano a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na kasar NNPC, Andrew Yakubu, wanda shi ma wani ne ya tona musu asiri. Alhaji Lai Mohammed ya ce daga cikin kudin, dala miliyan dari da talatin da shida da dubu dari bakwai, an gano su ne a wani banki a kasar, an an boye su ne da wani suna na bogi. Ya ce naira biliyan bakwai kuma da dala miliyan goma sha biyar, an same su ne daga wurin mutun guda, sai kuma wata naira biliyan daya da aka samu daga wajen wani mutun guda shima. Ministan ya ce wannan bankadowa da aka yi, ta kara jaddada matsayarsu a baya, cewa an tafka babbar sata a zamanin tsohu...
Comments