Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ta dauki wasu matakai domin rage farashin kayan abinci.

Ministan albarkatun gona, Mista Audu Ogbe shi bayyana hakan ga manema labarai a yau Laraba bayan kammala taron majalisar koli ta kasa da aka gudanar.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata gwamnati ta kafa kwamiti na musamman domin duba yiwuwar rage farashin kayan abinci.
Mista Ogbe ya ce kwamitin ya gabatar da rahotonsa ga majalisar a yau. Sannan ya kara da cewa kwamitin ya gano cewa ba wai karancin abinci bane ya jawo tsadar kaya illa tsadar kudin motocin da ake jigilar kayan abincin da su.
Ya kara da cewa ana jigilar kayan abinci a manyan motoci wadanda suke amfani da man gas wanda kuma kowa yana sane da cewa gas ya yi tsada, wanda hakan ne ya jawo farashin kayan abincin suka yi tashin gwauron zabi. Ya ce don hakka za a soma amfani da jiragen kasa wajen safarar kayan abincin.
Ministan ya kara da cewa soma amfani da jirgin kasa da aka yi wajen safarar shanu daga yankin Arewa zuwa jihar Lagos ya taimaka wajen rage tsadar dabbobi, don haka za a yi amfani da irin wannan tsarin wajen jigilar kayan abinci.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya