RIKICIN KUDANCIN KADUNA: An Sake Kashe Mutane 21 A Kaura Da Jemaa

Shugaban karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna Mista Alex Iya, ya tabbatar da kisan mutane 14 a wani tagwayen hare-hare a kauyukan Mifi da Ashim da wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani suka kai a safiyar yau Litinin.
Rahotanni daga karamar hukumar Jema’a na cewa, a daren jiya aka kai wani hari inda aka kashe mutane bakwai a unguwar Bakin Kogi da ke cikin karamar hukumar ta Jema’a.
Dan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar karamar Hukumar Kaura, Dakta Yakubu Bityong ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda harin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 21 a yankin kudancin Kaduna, ya kuma ce, maharan sun kone gidajen jama’a da dama kafin zuwan jami’an tsaro yankin.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya