Jamiyyar APC Ta Nada Kwamiti Domin Shirya Ganduje Da Kwankwaso
Uwar jam’iyyar APC ta nada wata kwamiti domin shirya wadansu ‘ya’yanta da ba sa ga maciji a tsakaninsu.
Jam’iyyar ta ce ta yi hakanne domin hada kan ‘ya’yan jamiyyyar a jihohin da ake da matsaloli tsakanin jiga-jigan ‘ya’yan nata.
Akalla jihohi 12 ne jam’iyyar ke fama da irin wadannan matsaloli.
Rikicin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai da sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani da kuma jihar Kano tsakanin gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun fi muni a cikin su.
Kakakin Jam’iyyar APC din Bolaji Abdullahi, yace jam’iyyar ta na so ta ga cewa ta dinke duk wata baraka ce da take neman hadiye’ya’yan jam’iyyar a ko’ina a fadin kasar nan ganin cewa za’a gudanar da babban taron jam’iyyar a watan Afurilun wannan shekaran.
Wadansu jihohin da ake samun irin wadannan matsaloli sun hada da jihar Kogi, Adamawa, Nasarawa, Bauchi, Bayelsa, Zamfara da saurasu.
Comments