Za A Dauki Karin Wasu Matasa Dubu 350 A Nijeriya
Ofishin mataimakkin shugaban Najeriya ya ce za a dauki karin wasu matasa dubu 350 da suka kammala karatu a karkashin shirin nan da aka yi wa take N-Power, bayan da aka dauki wani adadi na mutane dubu 200 karkashin kasafin kudi na shekarar bara.
A karkashin wannan shiri dai matasan na gudanar da ayyuka ne a fanni guda uku, wato aikin malanta, kiwon lafiya da kuma aikin gona.
Shirin na ci gaba da samu goyan baya a wasu jihohin kasar tareda yi tasiri a wadannan fannoni.
Comments