Kashi 20 Cikin 100 Na Kudin Nigeria jabu ne - Dr Obadia Mailafiya

Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun ce kimanin kashi 20 cikin 100 na tsabar kudin da ake kashewa a kasar na jabu ne.
Daya daga cikinsu, Dr Obadia Mailafiya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa hakan na barazana ga tattalin arzikin kasar, wanda tuni ya fada mawuyacin hali.
A cewarsa ma'aikatan babban bankin kasar na hada baki da bankunan kasuwanci domin sake dawo da kudaden da suka tsufa cikin sha'anin hada-hadar kudi.
Dr Mailafiya ya ce, "idan kudade suka tsufa akan tara su ne a kone, sannan a kera wadanda za su maye gurbinsu. Amma akan samu ma'aikatan babban banki su hada baki da bankunan kasuwanci inda za a sake mayar da kudin cikin harkokin kasuwanci."
Tsohon mataimakin shugaban babban bankin na najeriya ya ce an shafe fiye da shekara ana yin hakan, yana mai cewa idan aka ci gaba da wannan cuwa-cuwa babu ta yadda naira za ta sake tagomashi a kan dala.
Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta yi sauye-sauye kan yadda take kera naira ta yadda ba za a yi saurin iya yin jabunta ba, sannan kuma zai yi wuya a dawo da kudin da ya lalace cikin harkokin hada-hada.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya