Gambia Ta Yabi Najeriya Kan Rawar Da Taka a Kasar
‘Yan majalisar sun yabawa kasashen Najeriya, Liberia, Ghana Saliyo da Senegal, bisa tsayin daka da suka yi wajen gyara al'amura a kasar Gambiya biyo bayan turjiyar da tsohon shugaba Yahya Jamme ya yi na kin sauka daga mulki duk da shan kaye da ya yi a zabe.
Dan majalisar ta ECOWAS daga kasar ta Gambiya Alhaji Seini Abdoullaye ya ce bisa taimakon Shugaba Muhammdu Buhari da ya yi ta kai komo tsakanin Abuja da Banjul, yau gashi an gyara al'amura a Gambia.
Dan majalisar dokokin kasar Gambiya Alhaji Mohammed Bah, ya ce Najeriya uwace mai ba da mama a nahiyar Afirka musamman in aka yi la'akkari da irin rawar da take takawa a nahiyar Afirka.
Najeriya ta kashe sama da Dala biliyan 50 wajen samar da zaman lafiya a kasashen Laberia da Saliyo kana tana jan gabarar gyara duk wasu al'amura a Afrika ta na ma yin amfani da albarkatunta don haka ta cimma ruwa.
Comments