Kungiyar Kwadago Za Ta Yi Zanga Zanga Bisa Halin Da Kasa Ke Ciki
Kungiyar Kwadago ta Kasa ta shirya gudanar da
zanga zangar nuna rashin Jin dadi game da
yanayin kunci da al'ummar Nijeriya ke ciki tare
kuma da neman karin albashi daga gwamnatoci.
Shugaban Kungiyar, Kwamred Ayuba Wabba ya ce
a ranar Alhamis ne za a gudanar da zanga zangar
a biranen Legas da Abuja inda kungiyar za ta
gabatar da jerin bukatunta ga Fadar Shugaban
kasa da majalisar tarayya. Ya kara da cewa za a
fadada zanga zangar zuwa jihohi.
Comments