Buhari Ya Tattauna Da Trump Ta Waya
Shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta wayar Tarho a yau da misalin karfe 3:45 na yamma agogon Najeriya. Buhari ya tattauna da Trump ne daga muhallinsa da ya ke hutu a London.
Sannan Trump zai kuma tattauna da shugaban Afrika ta kudu Jacob zuma bayan ya tattauna da Buhari ta wayar tarho.
Malam Garba Shehu mai magana da Yawun shugaban Najeriya ya ce shaidawa RFI hausa cewa tattaunawar tsakanin shugabannin biyu ta mayar da hankali ne a game hulda tsakanin Amurka da Najeriya.
Wannan ne dai karon farko da Shugaban Amurka Donald Trump zai tattaunawa da shugabannin Afrika tun rantsar da shi a watan Janairu.
Comments