Lauyan Buhari ya nesanta shugaban daga bai wa alkali Adeniyi kyautar naira 500,000

Lauyan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nesan ta shugaban daga zargin bai wa wani alkali Adeniyi Ademola kyautar naira 500,000.
Wani shaida da ya bayyana a gaban kotu a shari'ar cin hanci da ake yiwa alkali Ademola ya ce Buhari ya bai wa Lauyan kyautar kudin a dai dai lokacin da alkalin ke sauraron tuhumar da ake yiwa shugaban na rashin mallakar shaidar kammala karatu.
Lauyan Buharin Kola Awodein ya ce daga aljihun sa ya bai wa mai shari'a Ademola kudin a matsayin gudumawar auran 'yar sa da aka yi a Lagos.
Awodein ya ce ba da sanin Buhari ya yi kyautar ba kuma babu hannun sa a ciki.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya