Nigeriya Za Ta Kawo Karshen Tsadar Abinci Cikin Gaggawa
A Najeriya, wata sanarwa daga ofishin mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ta ce kwamitin cika aiki da ya kaddamar a taron ministocin da aka yi a kasar ranar Laraba 1 ga watan Fabrairun 2017, ya yi tattauanwarsa ta farko da safiyar Juma'a.
Tattaunawar da mukaddashin shugaban kasar ya jagoranta, ta mayar da hankali ne a kan yadda za a fahimci matsalolin da suka haddasa hauhawar farashin kayayyaki a kasar, musamman a kasuwannin fadin kasar.
Sanarwar ta ce kwamitin ta duba hanyoyin da za a bi domin kawo karshen matsalar cikin gaggawa, inda ta mayar da hankali kan samar da kayayyaki kuma cikin farashi mai rahusa.
Kwamitin ya kuma duba wasu nau'o'in abinci da jama'a suka fi amfani da su, da kuma dalilin da ya sa farashinsu ya hau a kasuwa cikin wasu yankunan kasar, duk kuwa da cewa manoma sun samu albarka a damunar bana.
Cikin matsalolin da suka gano har da rashin hanyoyi masu kyau da wuraren karbar haraji a kan hanyoyin, da rashin hanyoyin rarraba kayan noma, da ma wasu abubuwa da ke da alaka da tsadar sufuri.
Kwamiti cika aikin dai ya ce gwamnati za ta sanya hannu domin tabbatar da kawar da abubuwan da ke kawo tarnaki.
Amma kuma kwamitin ya jaddada cewa ba wai gwamnati za ta yi katsalandan ne cikin harkokin kayan abinci a kasuwa ba, ko kuma ya kayyade farashin sayen abincin da jama'a suka fi amfani da su.
Comments