Mu ma za mu fito zanga zanga domin nuna goyon bayan mu ga Buhari – Kungiyar ‘Ina tare da Buhari’
Kungiyar ina tare da Buhari wato ‘#IstandwithBuhari’ ta sanar da cewa ita ma ta shirya fitowa zanga zanga domin nuna goyon bayan ta ga shugaba Muhammad
u Buhari.
Kungiyar tace zata fito ranar 5 da 6 ga watan Faburairu.
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su fito domin nuna goyon bayansu ga shugaba Muhammadu Buhari akan ayyukan da yake yi na cigaban kasa Najeriya.
Rundunar ‘yansanda ta shawarci mawaki Tuface da ya dakatar da fitowa zanga zangar da ya ke shirin yi domin nuna rashin jin dadinsa akan mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Comments