El Rufai Ya Haramta Jamian Kiyaye Hadurra Kan Titinan Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta fatattaki hukumar kare haddura ta kasa daga gudanar da wata aiki a jihar.
Gwamnatin ta ce tayi hakanne a dalilin rahotanni da take samu cewa ma’aikatan hukumar na muzguna wa masu abin hawa a jihar.
Ta kara da cewa ma’aikatan hukumar su koma manyan hanyoyi domin yin aikinsu kamar yadda take a dokat kasa.
Bayan haka kuma gwamnatin jihar ta san ya dokar hana manyan motoci masu daukar mai su yi dakon kayan miya wato tumatur ko itace a saman motocin dakon man.
Gwamnati tace duk motar da aka kama daga yanzu na aikata hakan za’a hukuntashi.
Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan bayan kammala taron da kwamitin tsaron jihar tayi a fadar gwamnati dake Kaduna.
Comments