Hotuna: Jami’an Yan Sanda Sun Hana Masu Zanga-zanga Zuwa Fadar Shugaban Kasa
Kamar yadda aka sani ne cewa yau wadansu kungiyoyi a Najeriya musamman a jihohin Legas, Fatakol, da babban birnin tarayya, Abuja sun fito domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu akan yadda gwamnatin Buhari ke tafiyar da sha’anin mulki a kasar, daga Abuja gungun ‘yan zanga-zangar sun taru ne a matattaran Unity Fountain in da suka dunguma zuwa cikin gari Abuja.
Jami’an ‘yan sanda sun dakatar da su a hanyar su ta zuwa fadar shugaban kasa din.
Wani jagora a cikin su mai suna Chidi Odinkalu yace ya zama dole su fito domin a nemi sanin inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake da kuma halin da ya ke ciki a yanzu.
Yace mutanen kasa na fama da wahala sannan kuma shugaban kasa ya tafi wata kasa babu takammamen labari akansa.
“ Wasu sunce ya Buhari ya tafi hutu wasu kuma sunce a’a ya tafi ganin likita ne, mu kuma bamu san wanda za mu dauka ba.” Inji OdinKalu.
Yace babu wata doka da ta ce dole sai rundunar ‘yan sanda sun baka lasisi kafin ka gudanar da zang-zanga a kasa.
Comments