Jiragen Ruwa 26 Sun Iso Legas Makare Da Man Fetur Da Abinci
Jirage 26 ake tsammanin za su isa Apapa da Tin-Can Island makare da man fetur, abinci da sauran kayayyaki daga 14 ga watan fabrairu zuwa 27, na 2017.
Hukumar da ke kula da tasoshin ruwa ta Nijeriya NPA ta tabbatar da haka a mujallar ta ‘Shipping Position', a jiya.
Kuma ta tabbatar da 7 daga cikin jiragen na dauke da man fetur ne, kuma ragowar 19 na dauke da alkama, mai, sukari, gishiri, fulawa man girki da sauransu.
Comments