Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati za ta duba koke koken da masu zanga-zanga kan matsin tattalin arziki
Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati za ta duba koke koken da masu zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ta samu kanta a ciki da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
Tun da safiyar Litinin ne dai mutane suka fara taruwa a filin wasa na birnin Lagos, wurin da tuni aka baza jami'an 'yan sanda. Mutane suna dauke da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce a kansu kamar, "Mutane na fama da yunwa da rashin aikin yi, suna kuma cikin fushi."
Wasu kwalayen kuma an rubuta, "Ba zai yiwu a ce an bambanta hukuncin da ake wa talakawa da masu arziki ba." Kungiyar da ke jagorantar zanga-zangar mai suna Enough is Enough, ta ce ta fito ne domin nuna damuwa a kan al'amuran da suke damun jama'a kamar rashin tsaro da tabarbarewar bangaren ilimi da na lafiya da rashin wutar lantarki da kuma rashin aikin yi.
Comments