An gano gawar matashi rataye jikin bishiya a Tsamiya Babba, Kano -BBC Hausa
Ana zargin wani matashi mai kimanin shekara 30
ya rataye kansa a ƙaramar hukumar Gezawa ta
jihar Kano.
Da safiyar Alhamis ne aka wayi gari da ganin
gawar matashin rataye a jikin wata bishiya a
ƙauyen Tsamiya Babba.
Rundunar 'yan sandan Kano ta ce bisa dukkan
alamu matashin ne ya rataya kansa.
Sai da matashin ya cire tufafinsa tsaf sannan ya
rubuta "Nura", kuma ya ajiye tufafi da carbi da
takalmansa a ƙasan bishiyar da ya rataye kansa.
Mutanen ƙauyen Tsamiya Babba sun ce matashin
baƙo ne, don kuwa babu wanda ya san shi ko a
ƙauyukan yankin masu maƙwabtaka.
Ya zuwa yanzu ba a san daga inda matashin ya
fito ba, kuma ba a san dalilin da ya sanya shi
kashe kansa ba.
Ko a watan jiya ma an samu wata tsohuwa rataye
a jikin bishiya cikin ƙaramar hukumar Gezawa, 'yan
sanda sun ce suna gudanar da bincike a kan kisan
tsohuwar, wadda suka ce suna kyautata tsammanin
ba kashe kanta ta yi ba.
Mai magana da yawun 'yan sanda a Kano, DSP
Magaji Musa Majia, ya ce sun ƙaddamar da bincike
a kan ratayar matashin
Comments