Gwamnatin Najeriya ta amince da daukar sabbin 'yan sanda 10,000 duk shekara

Gwamnatin Najeriya ta bawa rundunar ‘yan sandan kasar, daukar sabbin jami’ai dubu goma a duk shekara, domin kawo karshen rashin yawan jami’an tsaron da kasar ke fuskanta.
Babban Sifeton ‘yan sandan kasar Ibrahim Idris ya tabbatar da samun cigaban, yayinda yake jagorantar wani taro da manyan jami’an ‘yan sanda a birnin Abuja.
Sifeto Janar Idris, ya ce Karin ya zama tilas domin samun nasarar murkushe aikata miyagun laifuka a kasar.
Ya ce kara yawan jami’an ‘yan sandan zai canza alkalumman da ke aiki a Najeriya, da ya nuna cewa dan sanda guda ne ke lura da mutane 400 a kasar.
A bangaren majalisar kasar kuwa, Sifeto Janar Idris ya bukaci da ta gaggauta sanya hannu kan kudurin da aka gabatar mata na kara yawan kudaden da ake warewa hukumar ‘yan sandan kasar.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya