Naira Ta Fara Farfadowa

Naira tana ci gaba da farfadowa da faduwar da darajarta ta yi a kasuwar canji ta bayan fage, bayan daukar matakin sauya tsarin tabbatar da wadatuwar dalar Amurka da babba bankin Najeriya yayi a ranar Litinin.
A ranar Talatar da ta gabata an saida dalar Amurka 1 kan naira 510 daga 520 da aka saida ranar Litinin. A ranar Laraba kuwa an saida dalar ce kan naira 505, yayinda a jiya Alhamis aka saida dala daya kan naira 470.
A Litinin din da ta gabata ne dai babban bankin Najeriya CBN, ya bayyana sabon tsarin kara yawan dalar da zai saidawa masu bukata a kasar, inda a ranar Talatar da ta gabata bankin na CBN ya fitar da dala miliyan $500, inda bankunan kasar 23 suka sayi dala miliyan $371.
Daga cikin sabon tsarin da babban bankin Najeriya ya fitar dai shi ne maida hankali wajen saidawa sauran bankunan kasar dalar, fiye da yan kasuwar canji ta bayan fage, domin karkatar da bukatar dalar da ake yi daga kasuwar zuwa wajen bankuna.
Kanana da manyan kwastomomin bankunan dai zasu rika sayen dalar kai tsaye, don biyan kudaden asibiti da kudin makaranta, sai kuma wadanda ke bukatar dalar domin fita kasashen waje.
Zalika a gefe guda a jiya Alhamis, Naira ta cigaba da farfado da darajarta kan fan din ingila, inda aka saida fan 1 kan naira 610 a maikon naira 645 a baya. Yayinda aka saida euro kan naira 507 a maimakon naira 537 a baya.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya