Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a jihar Neja a yau Talata.

Kakakin tsohon mataimakin shugaban kasan Paul Ibe ya ce Atiku ya ziyarci Babangida ne domin ya mika gaisuwarsa ganin cewa kwanan nan ne ya dawo daga asibiti.
Babangida ya dawo daga kasar Switzerland ranar Lahadi bayan makonni bakwai da ya yi a kasar ya na ganin likitoci.
Atiku ya koma garin Minna ne musamman domin ziyarar tsohon shugaban kasan saboda baya kasa a lokacin da ya je ta’aziyar rasuwar tsohon gwamnan jihar Abdukadir Kure a watan Janairun da ya gabata.
Daga karshe Paul Ibeh ya yi kira ga mutane da kada su yi ma wannan ziyara ta Atiku da wata fassara daban.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya