Kotu ta tabbatar da Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban PDP
Kotun wacce ke zaune a birnin Fatakwal, jihar Ribas, yau Juma’a 17 ga watan Febrairu tayi watsi da taron gangamin jam’iyyar da akayi 21 ga watan Mayun 2016, jaridar Tribune ta bada rahoto.
Alkalan guda 3 wadanda suka jagorancin karan sun amince da cewa Ali Modu Sherrif sahihin shugaban jam’iyyar.
Wannan hukunci zai kawo karshen rikicin shugabancin da ke damun jam’iyyar adawa ta PDP yayinda Sanata Ahmed Makarfi da Modu Sherrif suna ikirarin sune shugabannin jam’iyyar.
Markarfi da Sherrif sun zagaya kotuna a Legas, Abuja da Fatakwal amma karar yau ce ta karshe, Daily trust ta bada rahoto.
Kafin shari’ar yau, shugabannin guda 2 sun bayyana shirinsu da amincewa da sakamakon shari’ar kotun daukaka kara wanda zai kawo karshen rikici, ya kuma kawo zaman lafiya jam’iyyar.
Comments