Hukumomin zabe da na tsaro sun ce sun shirya tsaf domin gudanar da zabe a kananan hukumomin 11 dake jihar Gombe.

A jihar Gombe hukumomin zabe da na tsaro sun ce sun shirya domin gudanar da zabe a kananan hukumomin 11 dake jihar.
Rahotanni daga hukumomin biyu sun tabbatar da cewa an tanadar da duk abubuwan da suka wajaba domin gudanar da wannan zaben.
Mr. K.K Lubo, shi ne kwamishinan labarai da hulda da jama’a, a hukumar zaben jihar Gombe, ya kuma ce gobe da 8 na safe ya kamata a fara zabe, ana kuma sa ran cewa zai kai har karfe uku na yamma, inda ya bukaci jama’a bayan jefa kuri’a, su koma gida wadanda kuma suke da hakkin tsayawa su tsaya inda ya kamata su tsaya.
Ya kara da cewa kamar yadda jama’a ke ta kira cewa a yi amfani da na'urar tantance katin zabe ta “Card Reader” Mr Lubo, ya ce abinda aka saba amfani da shi a jihar da shi za ayi amfani domin a cewarsa Card Reader ba na Gwamnatin jiha bane na gwamnatin tarayya ne.
DSP Obet Mary, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar ta Gombe, ta ce hukumar a shirye ta ke domin ta tura ‘yan sanda kimanin 7,000 zuwa kananan hukumomi daban daban.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya