Wasikar Shugaba Buhari: Ba Zan Dawo Nijeriya Ba Har Sai Likitoci Sun Gamsu Da Lafiyata
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana
cewa ba zai dawo gida Nijeriya ba sai likitocin da
suke kula da shi a kasar Ingila sun ce sun gamsu
da lafiyarsa.
Buhari ya fadi hakan ne a wasikar da ya rubuta ma
shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki domin
sanar da majalisar neman karin kwananki domin
gudanar da gwaje-gwajen akan lafiyarsa a can
kasar na Ingila.
Majiyarmu ra PREMIUM TIMES ta samu cikakkiyar
wasikar da Buhari ya tura wa majalisar domin
sanar musu da hakan.
Buhari ya tafi hutu kasar Ingila inda yayi amfani da
hakan domin duba lafiyarsa.
Bayan kwanankin da ya dauka sun cika, ya rubuto
wa majalisar kasa domin neman karin kwanaki ya
ci gaba da zama a kasar har sai likitocin da suke
duba shi sun amince masa da ya dawo kasa
Najeriya.
Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne yake
ci gaba da zama a kujeran mulki na wucin gadi har
zuwa dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Comments