Yan Kasuwar Kano Sun Lalubo Bakin Zaren Dunkulewa
Domin kawo karshen matsalolin da kasuwanci da ‘yan kasuwar Jihar Kano ke ciki, yanzu haka masu ruwa da tsaki cikin harkokin Kasuwanci a jihar sun samar da wata kungiya irinta ta farko a tarihin kasuwacin Kano.
Kungiyar mai suna Gamayyar Kungiyoyin Kasuwannin Jihar Kano “Collations for Kano State Markets Association (KOKAMA), kungiyace da ta hade kungiyoyin kasuwanci a Jihar Kano sama da 60 don tabbatar da kawo gyara da kuma farkawa daga dogon barcin da ‘yan kasuwar Kano suka ce suna yi.
Yanzu haka kungiyar ta samar da iyaye biyu wadanda su ne aka amince za su iya cewa a yi ko a bari a farfajiyar kasuwanci a jihar wadanda su ne Alhaji Aminu Alhassan Dantata da Kuma Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu (Khadumul-Kur’an).
Da yake jawabi alokacin ziyarar da suka kaiwa Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu, Shugaban Gamayar Kungiyoyin ‘Yan Kasuwar Jihar Kano Alhaji Uba Zubairu Yakasai ya tabbatarwa da Khalifa Isyaka Rabiu amincewar ‘yan Kasuwan Jihar Kano su yi koyi da shi a bangaren kasuwanci.
“Muna sane da irin gudunmawar da ake bayarwa tun shekaru sama da sittin da suka gabata, musamman a lokacin da ake sauke kayan ‘yan Kasuwa a Legas. Duk Nijeriya Jihar Kano ce kadai ba ta da wani wanda zai ce a yi ko a bari ta fuskar kasuwanci, amma idan ka tafi kudancin kasar nan dama wasu jihohin arewacin Nijeriya za ka iske mutum guda ake karbar umarninsa, hakan na karawa wannan al’ummar daraja a idon abokan harkokinsu na yau da kullum”.
Da yake mayar da jawabi a lokacin ziyarar ‘yan kasuwar, Khalifa Isyaka Rabiu ya nuna farin cikinsa da Allah ya nuna masa wannan rana, ya ce “masu shekaru irin nawa duk sun kare, amma alhamdulillahi gashi yanzu kun taso kun zama manya wanda har kuka yi wannan hange mai kyau, saboda haka muna tabbatar maku da cewar mun amince da wannan bukata taku, kuma za mu yi bakin kokari domin ganin an samu natija a cikin wannan tsari.
“Muna sane da irin halin da kasuwanci da ‘yan kasuwa suka tsinci kansu a ciki, saboda haka duk wanda ya kamata mu yi magana da shi kan harkokin ci gaban ‘yan kasuwarmu za mu yi magana dashi kuma alhamdulillahi suna sauraronmu kwarai da gaske.
“Wannan kungiya ta zo a daidai lokacin da ake bukatar ta, muna fatan ‘yan Kasuwa kowa ya ci gaba da fitar da hakkin Allah daga cikin dukiyarsa (Zakka) a kuma dage da yin sadaka tana tsarkake dukiya kwarai da gaske”.
Ita ma Hajiya Fatima Sagir, shugabar mata ta wannan kungiya ta yi bayanin cewa cewa daga wannan lokaci idan Allah ya nuna mana shekara ta 2019 ‘yan kasuwa za su fitar da dan takarar Gwamna a Jihar Kano, “domin duk irin masu ilimin da ake bukata muna da su a cikin ‘yan kasuwarmu, sannan kuma mune muke da kaso mafi rinjaye na masu kada kuri’a, kuma muke bayar da kaso mai tsoka na gudunmawar kudade alokutan zabe, amma abin takaici an mayar damu ‘yan jagaliya, an daina daga wannan lokaci. Saboda haka kowa ya daura damarar yakin dawo da kimar ‘yan kasuwa da kasuwanci a Jihar Kano”.
Cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron akwai Alhaji Auwlu Gabari Jakada, Alhaji Gambo Muhammad Dan Pass, da wakilai daga Kasuwannin Sabon Gari, Kantin Kwari, Kwanar Singa, ‘Yan Katako rijiyar Lemo, Dawanau, Na’ibawa, ‘yan Lemo, ‘yan Kaba, Bayan Bompai, Kasuwar Rimi, Kadawa, Kasuwar Sheka, kasuwar wayoyin hannu da ke Farm Center da bakin Bata da sauransu.
Comments