Hotuna: Garin Da Ya Fi Ko Wane Gari Sanyi A Duniya
In har kana tsammanin tsananin sanyin da ka ke ji, ko ka taba ji, a garinku ko a wani wuri ya kai tsanani, to ka sake tunani.
Barka da zuwa Oymyakon, garin da ke arewacin Rasha, kuma garin da aka yi ittifakin ya fi ko wanne gari sanyi a duniya.
Tsanin sanyin Oymyakon, ya kai −71.2 °C a ma'aunin da aka auna a shekarar 1924.
A wannan watan na janairu, dumi da ka iya samu shi ne -50°C (-60°F).
Fitaccen mai daukar hoton nan na New Zealand, Amos Chapple, ya kai ziyara garin na Oymyakon.
Comments