A Karshe Dai Jamme Ya Mika Wuya, Ya Nemi Karin Wa'adin Awa 4
Tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya nemi karin lokaci daga 12 na rana zuwa 4 na yamma, don ya harhada kayansa ya yi gaba. Hakan na zuwa ne bayan dakarun ECOWAS sun tunkare shi gadan-gadan.
Wadansu majiyoyin gwamnatin kasar sun ce, ya yi wannan bukata ne lokacin da shugabannin kasashen Guniea da Mauritania suka isa Banjul, domin lallashin shugaban da ya sauka.
Comments