Najeriya Na Fuskantar Barazanar Yunwa A Bana
RFI Hausa
Najeriya na iya fuskantar yunwa a shekarar 2017 sakamakon Fari da rikicin makiyaya da manoma da na Boko Haram da kuma matsalar tattalin arziki a cewar rahoton hukumar FEWS da ke nazari kan Fari da wadarar abinci a duniya karkashin hukumar raya kasashe ta Amurka USAID.
Rahoton ya ce, za a fuskanci yunwa saboda yadda rikicin Boko Haram ya raba jama’a da gidajensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda ya gurgunta huldar kasuwanci tare da jefa halin ruyuwar jama’a cikin kunci.
Amma Sakataren kungiyar Manoma ta Njeriya, Alhaji Muhammad Magaji, ya ce ko za a samu yunwar ba kamar yadda ake zata ba.
A cewar Magaji, matsalar za ta fi shafar yankin arewa maso gabashi bayan shafe shekaru uku ba a yi noma ba a yankin sakamakon rikicin Boko Haram.
Najeriya dai na fama da matsalar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyen mai da kasar ke dogaro da shi.
Gwamnatin Buhari yanzu ta mayar da hankali ga bunkasa ayyukan noma domin rage dogaro da arzikin fetir.
Rahoton FEWS ya kuma ce kasashen Somalia da Sudan ta Kudu da Yeman na iya fuskantar irin wannan matsalar ta yunwa saboda rikicin da kasashen ke fama da shi.
Shugaban hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya Stephen O’Brien ya ce rikicin da ake samu a Yemen ya zama wani sila na fuskantar matsalar karancin abincin mafi girma a duniya.
Jami’in ya ce akalla kashi 80 na al’ummar kasar miliyan 14 ke bukatar agajin abinci, kuma daga cikin su miliyan biyu na cikin mummunar yanayi.
Comments