Yahya Jammeh Ya Ki Sauka Bayan Cikar Wa’adin Mulkin Sa

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya ki sauka daga karagar mulki duk da barazana da ya ke fuskanta daga Senegal da kasashen ECOWAS na yin amfani da karfi domin kawar da shi bayan cikar wa’adin mulkin shi.
A yau ake sa ran rantsar da Adama Barrow a Senegal wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disemba.
A jiya Laraba ne 18 ga watan Janairu wa’adin mulkin Jammeh ya kawo karshe, kuma ya ki sauka bayan ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da ya sha kaye.
Dakarun Afrika yanzu haka na shirin yin amfani da karfi domin dora Adama Barrow kan mafadan ikon Gambia.
Senegal ta ba Jammeh zuwa 12 na daren jiya ya sauka, bayan ta jibge dakarunta a kan iyakokin Gambia.
Mataimakiyar shugaban kasar Gambia Isatou Njie-Saidy ta yi murabus kafin cikar wa’adin Jammeh , kuma yanzu ministocinsa 6 ne suka yi murabus domin nuna rashin goyon bayansu ga zarcewar wa’adin mulkin shi.
Fargabar yaki ya sa daruruwan mutanen Gambia ne tserewa zuwa Senegal kamar yadda baki ‘yan kasashen waje da suka je yawon bude ido ke ficewa kasar.
Daga yau dai za a iya samun gwamnati biyu a Gambia bayan rantsar da Adama Barrow a ofishin jekadancin kasar a Senegal.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya