An Gudanar Da Zanga-zanga Lokacin Rantsar Da Trump
A kalla daya daga cikin kungiyoyin dake gudanar da zanga-zanga ta lalata wasu kayayyaki kan hanyarsu zuwa cikin birnin Washington a yau Juma’a, jim kadan kafin rantsar da zababben shugaba Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45.
A yayin da wasu masu zanga-zanga suka yi tasu cikin lumana a wasu wurare a nan Washington, wasu yan adawar Trump da suke tafiya cikin tsakiyar birnin sun karya tagogi, suka kifar da gwandunan shara, kuma suka tada tartsatsin wasan wuta.
Masu zanga zanga sun yi shigar bakaken kaya suna dauke da kwalaye masu rubutu, karka sake bambancin launin fata ya zama abin tsoro.
Yan sanda sun yi amfani da feshin barkonon tsohuwa domin canzawa masu zanga zangar hanya.
Wasu masu zanga zangar da yan jarida suka yi hira dasu, sun ce gwamnatin Trump zata yi tsaurin ra’ayi fiye da duk wata gwamnati a kasar kuma suna wannan abu ne don nuna jajircewa.
Comments