Gayyata zuwa Sambisa ta tayar da ƙura

Gayyatar da gwamnatin Najeriya ta yi wa 'yan kungiyar da ke fafutikar ganin an ceto 'yan matan Chibok, wato BBOG, zuwa dajin Sambisa ta janyo zazzafar muhawara.
Ita dai gwamnatin, a wata takardar gayyata da Ministan watsa labarai Lai Mohammed ya aikewa kungiyar, ta yi kira ga 'yan BBOG su aike mata da sunayen mambobinsu uku domin a tafi da su Dajin Sambisa su ga irin fafutukar da ake yi ta ceto 'yan matan na Chibok.
A cikin sanarwar, ministan ya yaba wa 'yan kungiyar ta BBOG bisa fafutukar da suke yi, yana mai cewa, "Domin jinjinawa fafatukar da kuke yi don ganin an ceto 'yan matan Chibok, muna so ku ba mu sunayen mambobinku uku domin zuwa yankin arewa maso gabas ranar Litinin, 16 ga watan Janairu".
A cewar Minista Lai Mohammed za a yi tafiyar ne da ministan tsaro, da na watsa labarai, da wasu 'yan jarida da babban hafsan sojin kasa, da kuma babban hafsan sojin sama. Da farko tawagar za ta fara zuwa Yola don ganin yadda rundunar sojin sama ke farautar 'yan matan na Chibok, sannan daga bisani su shiga jiragen saman yakin da ke shawagi a Dajin Sambisa.
'Wasan-ɓuya'
Sai dai a wata wasikar martani da ta aike wa ministan, kungiyar ta ce mabobinta sun gana sun kuma yarda da yin amfani da irin wannan dama don sanin halin da ake ciki a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.
Amma, a cewar wasikar, "Kafin a yi batun tafiyar, ya kamata mu yi taro da ku domin ku amsa mana wasu tambayoyi da ke damun mu. Muna so mai bai wa shugaban kasa shawara a kan sha'anin tsaro da ministan tsaro da babban hafsan sojin kasa da kuma babban hafsan sojin sama su halarci taron".
Kungiyar ta yi korafin cewa kwanaki kadan da suka gabata wata kungiya da ta rika cin mutuncin su ta samu tarba ta musamman daga babban hafsan sojin kasa na Najeriya, lamarin da, a cewar ta, yake matukar damun ta.
Ta kara da cewa dole ne babban hafsan sojin ya nemi gafara daga wurinta sannan ya wanke kansa daga cin zarafin da kungiyar ta yi musu idan ana so su amsa goron gayyar gwamnati.
Daga bisani kuma daya daga cikin jagororin kungiyar, Aisha Yesufu, ta wallafa a shafinta na Twitter cewa tana kalubalantar shugaban kasar, Muhammadu Buhari, ya jagorance su zuwa dajin na Sambisa idan da gaske ne yake yaki da ta'addanci.
Batun dai ya sa wasu na ganin 'yan kungiyar ta BBOG suna kokarin guje wa gayyatar da aka yi musu ne kawai, inda wasu ma ke ganin da ma fafatukarsu ba ta wuce Abuja, fadar gwamnatin kasar, ba.
Sai dai wasu sun ce ba haka batun yake ba.
www.bbc.com/hausa/38628555

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya