Trump ya haramta zub da Ciki
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar haramta taimakawa kungiyoyin agajin da ke goyan bayan zub da Ciki, batun da tuni ya raba kan Amurkawa.
Mai Magana da yawun shugaban Sean Spicer ya ce, shugaban ya bayyana karara cewar shi baya goyan bayan zub da Ciki, saboda haka zai kare lafiyar Amurkawa har ma da wadanda ke ci-ki.
Dokar ta shafi kungiyoyin agajin kasashen waje da ke samun tallafin kudade daga gwamnatin Amurka dan taimakawa masu bukatar zub da cikin.
Dokar na zuwa ne kwananki Biyu, bayan mata sun gudanar da jeren gwano a birnin Washington, kan kare hakkinsu cikin hada zub da ciki.
Shekaru 44 kenan da kotun kolin Amurka a karkahsin Alkali Roe Wade ta halarta zubar da cikin a shekarar 1973.
Tuni yunkurin shugaba Trump ya jawo kace-nace tsakanin iyalai da kungoyoyin kare hakkin mata da ke gani da sake.
A cewar Cecile Richard ta kungiyar kare hakkin matan kasar, dokar za ta fi tasiri kan mata marasa karfi, da ruguza tsari kayyade iyali.
''Babu mamaki idan a karshan wannan makon miliyoyin mata da maza sun fito bore adawa da wannan doka''.
Dama dai Amurka ce ke bada kaso mafi girma ga kungiyoyin da ke marawa zub da ciki baya da kayyade iyali a duniya.
Comments