Zan bar mulki don kauce wa zub da jini - Jammeh
Dazu-dazu nan ne shugaban kasar Gambia da aka kayar a zabe Yahaya Jammeh ya bayar da sanarwa da bakinsa cewa cewa ya yanke shawarar barin mulki bayan wata tattataunawar karshe da shugabannnin kasashen Afrikata Yamma 2.
A cikin wani takaitaccen jawabi da ya yi ta gidan tallabijin din kasar Sheikh Jammeh ya ce '' Ina ganin bai zama dole a zubar da ko da digon jini daya ne ba kan wannan batun.''
Sai dai bai yi karin bayani ba kan ko sun kulla wata yarjejeniya ba, kuma ba ta bayyana ba ko yaushe ne Adama Barrow - wanda ya doke shi yayin babban zaben kasar na watan jiya - zai koma kasar daga Senegal ya karbi mulki ba.
A cikin daren ranar Jumu'a dai, Barrow din ya yi sheda wa wani taron 'yan kasarsa a Dakar cewa '' zamanin mulkin tsoro a kasar Gambia ya kare.''
Jim kadan dai kafin jawabin na Jammeh, Shugaban kasar Mauritania Mohammed Ould Abdel'aziz - wanda ke aikin sasantawar na karshe - ya shaida wa manema labarai cewa an cima yarjejeniya kuma Jammeh zai bar kasar.
Wani jami'in fadar shugaban kasar ta Gambia wanda ke da masaniyar me ake ciki ya ce Yahaya Jammeh zai bar kasar ne a cikin kwanakki ukku , mai yiwuwa ma wani lokaci a yau Assabar tare da Shugaban kasar Guinea Alpha Conde wanda ya kwana a babban birnin kasar Banjul.
Jami'in dai ya nemi kamfanin dillacin labarai na AP da ya zanta da shi da ya sakaya sunansa saboda bai iznin yin magana da manema labarai a hukumance.
A jawabinsa na farko don kama mulki Shugaba Adama Barrow ya ce: "Daga yau (Alhamis), Ni ne shugaban ƙasar Gambia ko ka/kin zaɓe ni ko ba ka/ki zaɓe ni ba."
Ya ce "Wannan nasara ce ga ƙasar Gambia.. mulki a hannun jama'a yake a Gambia"
A cewarsa "Wannan rana ce wadda babu wani ɗan Gambia da zai taɓa mantawa da ita... karon farko tun bayan samun 'yancin kai, Gambia ta sauya gwamnati ta hanyar ƙuri'a".
Shugaban ƙasa biyu
A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh a kan mulki ya ƙare, ko da yake majalisar dokokin ƙasar ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.
'Yan Gambia da ma 'yan kasashen waje da ke zuwa yawon bude ido a kasar da yawa ne suka fice zuwa wasu ƙasashe maƙwabta saboda tsoron ɓarkewar rikici.
Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da aka yi cikin watan Disamba.
Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben.
Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben.
Comments