Ba zan fasa korar Musulmi daga Amurka ba —Trump
Gwamnatin Donald Trump ta tsaya kai da fata a kan aiwatar da matakinta na korar 'yan gudun hijira daga kasashen nan bakwai duk da hukuncin da wata kotu ta yanke na dakatar da shirin da kuma zanga-zangar da ake yi a kan matakin.
Mr Trump ya wallafa shafinsa na Twitter cewa Amurka na bukatar "tsattsauran mataki" yanzu kan 'yan gudun hijira.
Shugaban ma'aikatansa ya ce mutum 109 ne kawai cikin mutum 325,000 da suka yi balaguro aka tsare.
Wasu alkalai sun yanke hukunci a kan wannan batu - daya daga cikinsu, alkalin babbar kotun kasar ya dakatar da matakin hana masu izinin shiga kasar zuwa wani dan lokaci.
Kasashen duniya da dama sun yi tur da wannan matakin.
A ranar Juma'a ne dai Mr Trump ya sanya hannu a kan wasu shirye-shiryensa da suka hana bai wa 'yan gudun hijira izinin shiga kasar nan da kwana 120, sannan aka haramtawa 'yan gudun hijirar Syria shiga Amurka kwata-kwata, kana aka dakatar da 'yan kasashe bakwai na Musulmi daga shiga kasar tsawon kwana 90.
An tsare mutanen da ke kan hanyarsu ta komawa Amurka a lokacin da Mr Trump ya bayar da umarnin.
Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da aka juya da su ba daga filin jiragen sama a lokacin da suke son zuwa Amurka.
Dubban mutane ne suka taru a filayen jiragen sama daban-daban ranar Asabar, domin bijirewa matakin da gwamnatin Trump ta dauka kan Musulmin.
Comments