Trump Na Gab Da Hana Baki Shiga Amurka

A wannan larabar ake saran shugaban Amurka Donald Trump zai sanya hannu kan dokokin takaita shigar baki kasar kamar yadda ya bayyana lokacin yakin neman zabensa.
Rahotanni sun ce dokokin za su takaita bai wa bakin da suka fito daga kasashen Iraqi da Iran da Libya da Somalia izinin shiga Amurka.
Sauran kasashen da dokar zata shafa sun hada da Sudan da Syria da Yemen
A sakon da Trump ya aika ta kafar twitter ya ce lallai za su gina katangar da ya yi alkawari tsakanin Amurka da Mexico.
Kasa da mako guda da kama aiki, Mista Trump, ya aiwatar da muradai da dama sune jigo a yakin neman zaben da ya kayar da Hillary Clinton.
Shugaba Trump ya ce aikinsa shi ne kare Amurka da muradunsu.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya