Shugaban Mexico Yace Kasarsa Ba Zata Biya Kudin Wata Katanga Ba
Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto yace duk da yake yana fata su samu kyakkyawar dangantaka da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump amma kuma kasar sa bata da niyyar biyan kuddin gina wata katangar akan iyakar dake tsakanin kasashen nasu biyu.
Neito yace dukkan batutuwan dake tsakanin kasashen biyu da suka hada da batun tsaro,’yan gudun hijira, kasuwanci, duka abubuwa ne da yake shirye a zanta a kansu a tsakanin kasashen nasu, amma yace batun Mexico ta biya kudin ginin Katangar da trump ke son ganin an gina don hana bakin haure shiga Amurka, wannan batu ma bati taso ba.
Yace ba zasu taba yin na’am da duk wani abinda zai zubar da mutunci da kimarMexico a idon duniya ba.
Da kuma ya koma kan barazanar da Trump yayi na cewa duka kanfanonin da suka koma kasar ta Mexico za’a kara musu haraji muddin suka yi kokarin sayar da kayayyakinsu a Amurka, Pena Neito yace tuni yayi fatali da wannan barazanar ta tsorata masu zuba jari don a razana su.
Duk da haka, shugaban na Mexico dake shirin ganawa da Trump nan bada jimawa ba, yace yana fatar za su karfafa dankon dangantakar dake tsakanin kasashen nasu, musammam ta fannoninbunkasa harkokin kasuwanci.
Comments