Ya Mutu Wajen Satar Fetur
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Mr Rasak Fadipe, ya bayyana cewar sun tsamo gawa daga cikin ramin tankar mai a ranar talata.
Mr Fadipe ya ce an ajiye motar tankin ne daura da ofishin 'yan sanda na Morogbo a titin Badagry, inda kuma a ke kyautata zaton mutumin ya bude ramin tankar ne da nufin ya saci man, kuma ya rufta ciki ya mutu.
Comments