Mace daya cikin 10 na jin zafi lokacin jimai

Wani bincike da masana kimiyya suka yi ya nuna cewa kusan kowacce mace daya cikin mata 10 na matukar shan wahala a lokacin da ake yin jima'i da su.
Binciken da aka yi kan kusan mata 7,000 'yan tsakanin shekara 16 zuwa 74, wanda aka wallafa a mujallar Birtaniya mai suna British Journal of Obstetrics and Gynaecology , ya ce wannan matsala, wacce a kimiyyance aka sanya wa suna dyspareunia - ta zama gama-gari kuma tana shafar mata manya da kanana.
Sai dai binciken ya nuna cewa lamarin ya fi faruwa ga matan da suka haura shekara hamsin da doriya zuwa sittin da kuma 'yan tsakanin shekara 16 zuwa 24.
Amma likitoci sun ce ana iya magance matsalar.
Ana alakanta jin zafi lokaci jima'i da wasu matsalolin da suka danganci jima'i kamar bushewar farji da fargaba lokacin jima'i da kuma rashin jin dadin jima'in.
Wasu matan sun ce suna tsoron yin jima'i ne saboda suna matukar jin zafi.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya