Sojojin Senegal sun doshi Gambia
Wasu Majiyoyi sun tabbatar da ganin sojojin Senegal a kan iyakar Gambia a yau Laraba a wani mataki na shirin yaki da Yahya Jammeh bayan ya ki amincewa ya mika mulki ga Adama Barrow wanda ya lashe zaben kasar.
Gambia ta kama hanyar fadawa cikin yaki tsakanin dakarun Yahya Jammeh da dakarun kasashen yammacin Afrika.
Daruruwan mutanen Gambia ne suka fice kasar zuwa Senegal kamar yadda baki ‘yan kasashen waje da suka je yawon bude ido ke ficewa.
Senegal da ke kewaye da Gambia, Rahotanni sun ce dakarun kasar sun doshi arewacin Gambia zuwa yankin Casamance a kudancin kasar.
A yau ne wa’adin Jammeh ke kawo karshe a matsayin shugaban Gambia bayan ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Disemba.
Kungiyar ECOWAS da ke matsin lamba ga Jammeh, ta ce za a rantsar da Barrow a wani yanki na Gambia ba lalle sai Banjul ba fadar gwamnatin kasar, matakin da ke nuna za a samu hedikwatar gwamnati biyu a kasar.
Rahotanni sun ce yanzu haka Najeriya na shirin tura dakaru 200 a Gambia inda tuni ta aika da jirgin ruwan yakinta a kasar.
Comments