Trump: Za mu fifita Kiristoci a kan Musulmi
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko a kan Kiristoci 'yan gudun hijira na Syria fiye da takwarorinsu Musulmi.
Mista Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin a ranar Juma'a, inda ya ce za su fi karbar Kiristocin 'yan gudun hijira da suka mika bukatar karbarsu a Amurka.
Shugaban ya kuma lashi takobin hana shiga Amurka ga Mutanen da suka fito daga wasu kasashe bakwai na Musulmi.
Mista Trump ya sanya hannu a wasu dokoki ranar Juma'a da ya ce za su kare Amurka daga tsattsauran ra'ayin kishin Islama.
Ya sanya hannun ne a kan dokokin ne bayan bikin rantsar da Janar James Mattis a matsayin sakataren tsaro a fadar gwamnatin Amurkar, White House.
Daga cikin dokokin a yanzu Mista Trump ya haramta wa 'yan gudun hijira na Syria shiga Amurka, har sai abin da hali ya yi.
Sannan kuma dokokin sun dakatar da bayar da takardar izinin shiga Amurka ga 'yan kasashen Iran da Iraq da Somalia da Sudan da Libya da kuma Yemen, har tsawon wata uku.
A lokacin yakin neman zabensa Mista Trump ya nemi da a hana Musulmi gaba daya shiga AmurkA.
Ya ce ya yi hakan ne a matsayin wani mataki na raba Amurka da masu tsattsauran kishin Musulunci.
Matakin na Shugaba Trum na ci gaba da samun kakkausar suka daga masu mara baya ga 'yan gudun hijira.
'Yar majalisar dattawan Amurka ta jam'iyyar Democrat Elizabeth Warren ta kira dokokin cin amanar al'adu da dabi'un Amurka.
Ita kuwa hadakar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta Amurka ta American Civil Liberties Union, ta ce dokokin rufa-rufa ce kawai na nuna wariya ga Musulmi.
Comments